'Yancin Jima'i

Hakkin Yin Jima'i
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na Hakkokin Yan-adam
Hakkin yin Jima'i a tsakanin bil'adam
Shagon siyarda kayan jima'i

'Yancin jima'i ya ƙunshi 'yancin bayyana yanayin sha'awar mutum da kuma barranta daga duk wani tozarci dangane da yanayin sha'awar mutum na jima'i. A taƙaice dai, ya ta'allaƙa ne akan mutanen da ke da halin sha'awar jima'i daban daban, wanda suka haɗa da 'yan maɗigo, 'yan luwaɗi, masu sha'awar duka jinsi biyu (maza da mata) da kuma masu sauya halitta (LGBT), da kuma kare waɗannan haƙƙoƙi duk da cewa sun haɗa da 'yancin jima'i tsakanin namji da kuma mace. 'Yancin jima'i da kuma barranta daga tozarci ta fuskar yanayin sha'awa na daga cikin wanzuwar ɗan-Adam da kuma haƙƙoƙin da duk wani mutum yake da ita ta fuskar halittar ɗan-Adam.

Babu 'yancin yin jima'i a bayyane a cikin dokar haƙƙin ɗan Adam na duniya ; sannan a maimakon haka, ana samunsa a cikin wasu kayan kare hakkin dan Adam na kasa da kasa da suka hada da Sanarwar Kare Hakkokin Dan Adam ta Duniya, Yarjejeniyar Kasa da Kasa kan Hakkokin Dan Adam da Siyasa da Yarjejeniyar Kasa da Kasa kan 'Yancin Tattalin Arziki, Zamantakewa da Al'adu .


From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Nelliwinne